Palasdinu : Abass Zai Yi Jinya Har Zuwa Ranar Litini
(last modified Mon, 21 May 2018 15:11:42 GMT )
May 21, 2018 15:11 UTC
  • Palasdinu : Abass Zai Yi Jinya Har Zuwa Ranar Litini

Shugaban Palasdinawa, Mahmud Abass, zai yi jinya har zuwa ranar Litini, sakamakon ciwan gaba da kuma zazzabi mai tsanani dake damunsa, bayan tiyatar kunne da aka masa a makon da ya gabata.

Kamar yadda wani jami'in Palasdinun wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP, ya ce Shugaban zai kwanta asibiti don jinya har zuwa ranar Litini, saidai ba tare da yin karin haske ba.

Wannan dai shi ne karo na uku a cikin mako guda da ake kwantar da Shugaban Palsdinawan a asibiti, bayan da aka masa karamin aikin tiyata a kunne a ranar Talata data gabata.

Kafin hakan dai Daraktan babban asibitin Ramallah, ya ce  binciken kiwan lafiya da aka wa shugaba Abbas dan shekaru 83, sun bada sakamako mai kyau don babu wani abun damuwa a cikin yanayin lafiyasar.

A shekara 2005 ne aka sake zaben shugaba Mahmud Abass a wani wa'adin mulki na shekaru hudu, saidai ya ci gaba da mulki saboda kasa gudanar da zabe saboda sabani na cikin gida da kungiyar Hamas, kuma har yanzu bai bayyana wanda zai gaje shi ba.