Kawancen Amurka Ya hallaka Mutum 12 A Siriya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i31074-kawancen_amurka_ya_hallaka_mutum_12_a_siriya
Kungiyar kare hakin bil-adama ta bangaren adawar Siriya ta sanar da hallakar mutum 12 a wani hari da jiragen kawancen Amurka suka kai wuraren sojojin kasar
(last modified 2018-08-22T07:01:52+00:00 )
May 24, 2018 06:49 UTC
  • Kawancen Amurka Ya hallaka Mutum 12 A Siriya

Kungiyar kare hakin bil-adama ta bangaren adawar Siriya ta sanar da hallakar mutum 12 a wani hari da jiragen kawancen Amurka suka kai wuraren sojojin kasar

Tashar talabijin din Mayadin ta nakalto kafar watsa labaran Al-i'ilamul harbi a wannan alhamis na cewa jiragen yakin kawancen Amurka sun yi lugudar wuta a sansanin sojojin kasar Siriya dake yankin Mahattatu-Saniyah dake gefen kudancen Dairu-zur na gabashin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 12.

Saidai a nasu bangare jami'an tsaron Amurka sun bayyana cewa babu hanun kawancensu a wannan hari.

Bayan kai hari, mayakan kungiyar ISIS sun kaiwa Sojojin Siriyan hari.wanda hakan ke nuna cewa akwai alaka tsakanin bangarorin biyu.

Majiyar tsaron Siriya ta sanar da cewa Sojojin Amurkan sun kwashe mayakan ISIS daga yankin a yayin da Sojojin Siriya ke kai musu farmaki domin tsarkake  kudancen Dairu-zur dake gabashin kasar ta Siriya.