Palasdinu : An Sallami Abass Daga Asibiti
May 28, 2018 11:09 UTC
An sallami shugaban Palasdinawa, Mahmud Abass, daga asibitin Ramallah bayan shafe kwanaki takwas na jinya.
Kafin sallamarsa dai an sha cece-kuce kan yanayin kiwan lafiyarsa da kuma batun wanda zai gashe shi.
Rahotanni sun ce shugaban Abass, ya fito daga asibitin da kafarsa, inda kuma ya yi wa 'yan jarida bayyanin cewa yana shirin komawa bakin aikinsa a ranar Talata.
An dai kwatar da Mista Abass mai shekaru 83, saboda ciwan nimuniya dake damunsa, bayan kwantar dashi har kusan sau biyar a asibiti a waccen mako da ya gabata.
Tags