Jiragen Yakin HKI Sun Kai Hare Hare A Gaza
Sojojin Haramtacciyar kasar Isra'ila sun kai hare hare da jiragen sama a kan wurare masu yawa a yankin Gaza a jiya Talata
Tashar talabijin ta Presstv a nan tehran ta nakalto kakakin sojojin HKI Jonathan Conricus yana fadawa yan jaridu a jiya Talata kan cewa sojojin HKI sun hare hare kan wuraren soje a cikin yankin Gaza mallakin kungiyar Hamsa da kuma Jihadul Islami.
Jonathan ya kara da cewa sojojinsa sun kai hare haren maida martani ne kan rokokin da mayakan Hamas da Jihadul Islami suka cilla cikin yankunan da HKI ta mamaye.
Labarin ya kara da cewa musayar hare hare tsakanin Palasdinawa da kuma Yahudawan Sahyiniya sun yi yawa,kuma rabon da ganin haka tun shekara ta 2014.
An fara tashe tashen hankula a yankin Gaza da kuma sauran yankunan Palasdinawan da haramtacciyar kasar Isra'ila ta mamaye ne tun ranar 14 ga watan Muyun da muke ciki wato a dai dai lokacinda HKI take bukukuwan kafata shekaru 70 da suka gabata. Har'ila yau a lokacin nne gwamnatin kasar Amurka ta dauke ofishin jakadancinta daga Telaviv zuzwa birnin Qudus.
Daga lokacin zuwa yanzu dai Palasdinawa da dama ne sojojin HKI suka kashe, sannan wasu da dama suka ji rauni.