Kungiyar Turai Ta Bukaci Sakin Fursunonin Siyasar Kasar Hadaddiyar Daular Larabawa
Shugaban Kwamitin kare hakkin bil-Adama a Majalisar Dokokin kungiyar tarayyar Turai ya bukaci sakin dukkanin fursunonin siyasa da ake tsare da su a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
Shugaban kwamitin kare hakkin bil-Adama a Majalisar Dokokin Kungiyar tarayyar Turai Pier Antonio Panzeri a jiya Litinin ya gabatar da bukata ga gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa kan hanzarta sakin Ahmad Mansur dan siyasar kasar da ake tsare da shi a gidan kurkuku gami da sauran fursunonin siyasa.
Tun a ranar Alhamis da ta gabata ce gwamnatin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta sanar da hukuncin daurin shekaru 10 a gidan kurkuku kan Ahmad Mansur tare da biyan tara na tsaban kudi dalar Amurka 272,000.
An kama Ahmad Mansur injiniya a fannin ilimin wutan lantarki kuma mawaki tun a watan Maris na shekara ta 2017 ne kan zargin neman tunzura al'ummar kasar tare da cin mutuncin mahukuntan Hadaddiyar Daular Larabawa.
Har ila yau a shekara ta 2011 Ahmad Mansur tare da wasu mutane biyar sun shiga hannun mahukuntan kasar Hadaddiyar Daular Larabawa kan zargin cin mutuncin mahukuntan kasar tare da sukar salon gudanar da siyasar kasa a shafinsu na sada zumunci a lokacin da al'ummar kasar suka yunkuro domin neman ganin an wanzar da tsarin dimokaradiyya a kasarsu.