An Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar Masar Bayan Karin Kudin Makamashi
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i31780-an_tsaurara_matakan_tsaro_a_kasar_masar_bayan_karin_kudin_makamashi
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ce ta sanar da tsaurara matakan tsaro saboda sa-ido akan duk wani yunkuri na nuna kin amincewa da karin farashin makamashi da aka yi
(last modified 2018-08-22T07:01:59+00:00 )
Jun 17, 2018 07:35 UTC
  • An Tsaurara Matakan Tsaro A Kasar Masar Bayan Karin Kudin Makamashi

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Masar ce ta sanar da tsaurara matakan tsaro saboda sa-ido akan duk wani yunkuri na nuna kin amincewa da karin farashin makamashi da aka yi

Sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta fitar ya kunshi cewa wuraren da aka girke jami'an tsaro sun hada da tasoshin jirgin kasa da gidajen mai da kuma sauran wuraren taruwar al'umma.

An sami fitowar masu Zanga-zanga a cikin birane da dama na kasar ta Masar da suke nuna kin amincewa da karin farashin makamashin, musamman iskar gas da aka yi a kasar.

Karin da gwamnatin kasar ta Masar ta yi a washe garin salla, yana tafiya ne a karkashin aiki da tsare-tsaren Asusun ba da lamuni na duniya.

Daga watan Nuwamba na 2017 zuwa yanzu sau uku kenan a jere gwamnatin kasar na kara kudin makamashi.