Rasha Ta Zargi Amurka Da Goyon Bayan 'Yan Ta'adda
Jun 20, 2018 12:11 UTC
Jakadan Kasar Rasha A Lebanon ne ya yi zargin cewa Amurkan tana taimakawa 'yan ta'adda a kasar Syria
Alexander zasypkin da tashar talabijin din almayaden ta yi hira da shi ya ce; Kasarsa ta shiga cikin kasar Syria ne bisa gayyatar gwamnatin wannan kasa.
Alexander zasypkin ya kara da cewa kasarsa tana goyon bayan tataunawar da ake yi a Geneva akan kasar ta Syria, sannan kuma ya yi watsi da cewa da akwai yarjejeniya a tsakanin kasarsa da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da makomar kasar Syria.
Jakadan na kasar Rasha ya kuma ce; Sojojin kasar syria suna kokarin tabbatar da tsaro a yankunan da su ke kudu da birnin Damascuss bayan da su ka sami nasara akansu a yankuna daban-daban.
Tags