Rasha Ta Zargi Amurka Da Goyon Bayan 'Yan Ta'adda
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i31876-rasha_ta_zargi_amurka_da_goyon_bayan_'yan_ta'adda
Jakadan Kasar Rasha A Lebanon ne ya yi zargin cewa Amurkan tana taimakawa 'yan ta'adda a kasar Syria
(last modified 2018-08-22T07:02:00+00:00 )
Jun 20, 2018 07:41 UTC
  • Rasha Ta Zargi Amurka Da Goyon Bayan 'Yan Ta'adda

Jakadan Kasar Rasha A Lebanon ne ya yi zargin cewa Amurkan tana taimakawa 'yan ta'adda a kasar Syria

Alexander zasypkin  da tashar talabijin din almayaden ta yi hira da shi ya ce; Kasarsa ta shiga cikin kasar Syria ne bisa gayyatar gwamnatin wannan kasa.

Alexander zasypkin ya kara da cewa kasarsa tana goyon bayan tataunawar da ake yi a Geneva akan kasar ta Syria, sannan kuma ya yi watsi da cewa da akwai yarjejeniya a tsakanin kasarsa da kuma haramtacciyar kasar Isra'ila dangane da makomar kasar Syria.

Jakadan na kasar Rasha ya kuma ce; Sojojin kasar syria suna kokarin  tabbatar da tsaro a yankunan da su ke kudu da birnin Damascuss bayan da su ka sami nasara akansu a yankuna daban-daban.