Bahrain Na Shirin Kulla Huldar Diflomatsiyya Da H.K Isra'ila
Shafin yanar gizo na labarai na I-24-News mallakin HKI ya bayyana cewa kasar Bahrain ce zata zama kasar Larabawa ta farko wacce zata samar da huldan jakadanci da HKI.
Jaridar Al-qudsul Arabi ta nakalto shafin I-24-News tana cewa wani babban jami'in gwamnatin kasar Bahrain, wanda ba'a bayyana sunansa ba yana cewa gwamnatin kasar Bahrai ba ta daukar HKI a matsayin makiyi, sannan kusanci tsakanin kasashen biyu bai sabawa manufofin gwamnatin kasar ta Bahrain ba.
A wane bangaren kuma ma'aikatar harkokin wajen HKI ta tabbatar da cewa wata tawaga ta musamman wacce zata hada da manya manyan jami'an gwamnatin kasar zata kai ziyarar aiki a kasar Bahrain a ranar 24 ga watan Yunin da muke ciki don halattan wani taron da hukumar UNESCO ta majalisar dinkin duniya za ta shirya raya al-adu..
Labarin ya kara da cewa wannan shi ne ziyara ta farko a hukumance wacce wata tawaga daga HKI take kaiwa daya daga cikin kasashen larabwa na yankin tekun farisa wacce babu huldan jakadanci a tsakaninsu.
Masana dai suna ganin mafi yawan kasashen Larabawa suna aiki tare da HKI a boye musamman abinda ya shafi cikin yake yaken da ke aukuwa a kasashen Siriya Iraki, Lebanon da kuma Yeman.