Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Kai Hari A Yankin Gaza
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32080-haramtacciyar_kasar_isra'ila_ta_kai_hari_a_yankin_gaza
Majiyar Palasdinawa ta tabbatar da cewa; Da safiyar yau Laraba jiragen yakin 'yan sahayoniya su ka kai hari akan wata motar Palasdianwa asansanin al-Nusairat da ke yankin Deir Balah.
(last modified 2018-08-22T11:32:02+00:00 )
Jun 27, 2018 07:25 UTC
  • Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ta Kai Hari A Yankin Gaza

Majiyar Palasdinawa ta tabbatar da cewa; Da safiyar yau Laraba jiragen yakin 'yan sahayoniya su ka kai hari akan wata motar Palasdianwa asansanin al-Nusairat da ke yankin Deir Balah.

Bugu da kari tashar talabijin din al-Mayadeen ta ba da labarin cewa sojojin Sahayoniyar sun kai wasu hare-haren da manyan bindigogi a arewacin Gaza.

Kawo ya zuwa yanzu babu cikakken bayani yawan asarar da hare-haren na 'Yan sahayoniya su ka kai.

A jiya talata ma dai 'yan sahayoniyar sun kai wani harin a arewa da gabacin yankin Gaza.

Tuni dai 'yan gwagwarmaya a yankin Gaza su ka gargadi haramtacciyar Kasar Isra'ila da mai da martani, matukar ta ci gaba da kai hari.