Masar Ta Rufe Mashigar Rafah
Cikin wani mataki na ba zata da hukumomin kasar Masar suka dauka sun sanar da rufe mashigar Rafah na tsahon kwanaki uku.
Kamfanin dillancin labaran Anatolie ya habarta cewa ofishin sadarwa na mashigar Rafah dake kudancin zirin Gaza ya sanar da cewa hukumomin kasar Masar sun bayar da umarnin rufe mashigar Rafah na tsahon kwanaki uku, wanda ya fara aiki a yau juma'a.
A cikin watan Ramadan da ya gabata ne hukumomin kasar Masar suka bude mashigar Rafah na tsahon wata guda, sannan kuma bayan watan na Ramadana suka sake kara wa'adin wata guda, to saidai kafin watan ya cika, hukumomin na Masar suka dauki wannan mataki na bazata.
Al'ummar yankin zirin gaza na Palastinu na bukatar bude wannan mashiga na dindin din, to saidai alakar dake tsakanin hukumomin kasar Masar da Haramtacciyar kasar Isra'ila ya hana Masar din amsa bukatar na Palastinawa.