Shugaban Palasdinawa Ya Ki Ganawa Da Manyan Jami'an Gwamnatin Amurka.
(last modified Sun, 01 Jul 2018 07:26:19 GMT )
Jul 01, 2018 07:26 UTC
  • Shugaban Palasdinawa Ya Ki Ganawa Da Manyan Jami'an Gwamnatin Amurka.

Kamfanin dillancin Labarun Anatoli ya nakalto cewa; Shugaba Mahmud Abbas Abu Mazin ya yi watsi da gayyatar ganawa da manyan jami'an Amurka biyu

Rahoton ya ci gaba da cewa mutanen biyu da shugaban na palasdinawa ya ki ganawa da su ne manzon musamman na shugaba Donald Trump a gabas ta tsakiya, wato Jason Greenblatt, sai kuma sirikin shugaban na Amurka wato Jared Corey Kushner.

Wani jami'in gwamnatin kwarya-kwaryar palasdinu da ya bukaci a sakaya sunanshi ya fadawa kamfanin dillancin labarun Anatoli cewa; Jami'an na Amurka sun bukaci ganin shugaban palasdinawan ne bayan fitowarsa daga asibiti amma ya ki lamunta.

Amurka dai tana kokarin tallata shirin sulhunta palasdinawa da 'yan sahayoniya wanda ake kira da yarjejeniyar karni. Palasdinawa suna bayyana shirin da cewa yana cike da take hakkokin Palasdinawa.