Zaman Farko Domin Rahoton Take Hakkin Bil Adama A Bahrain
Kwarraru kan kare hakkokin bil adama na majalisar dinkin duniya sun fara gudanar da zama domin binciken rahoton da aka gabatar kan take hakkokin bil adama a kasar Bahrain.
Tashar Lu'ulua ta bayar da rahoton cewa, kwararrun sun fara gudanar da zamansu na farko ne kan rahoton da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suka hardahada kuma suka mika shi ga kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, inda kwamitin ya mika shi ga kwararru domin dubi a kansa.
A zaman da kwamitin ya gudanar a cikin watan Yunin da ya gabata, ya zargi masarautar Bhrain da cin zarafin 'yan adam, tare da keta hakkokin 'yan kasa sabosa dalilai na siyasa.
Rahoton dai ya kunshe bayanai da suke tabbatar da cewa, masarautar Bahrain ta tsare da daruruwan mutane saboda ra'ayoyinsu na siyasa, ko kuma banbancin akida, daga cikinsu akwai malaman addini, 'yan siyasa, lauyoyi, da masu fafutukar kare hakkokin 'yan kasa, gami da likitoci da 'yan jarida da dai sauransu.
Haka nan kuma rahoton ya tabbtar da cewa akwai kananan yara da ake tsare da su ana azabtar da su a cikin gidajen kurkukun Bahrain saboda irin wadannan dalilai na siyasa ko banbancin mahanga ta addini.
Jami'an kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya sun bukaci ziyartar kasar ta Bahrain domin ganin halin da ake ciki, amma masarautar kasar taki amincewa.