Yunkurin Tsagerun Yahudawan Sahayiniyya Na Rusa Wani Bangaren Masallacin Qudus
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32238-yunkurin_tsagerun_yahudawan_sahayiniyya_na_rusa_wani_bangaren_masallacin_qudus
Masu gadin Masallacin Qudus sun rusa wani makircin tsagerun Yahudawan Sahyoniyya na rusa yankin Babu-Rahmah na Masallacin Qudus.
(last modified 2018-08-22T11:32:04+00:00 )
Jul 08, 2018 12:09 UTC
  • Yunkurin Tsagerun Yahudawan Sahayiniyya Na Rusa Wani Bangaren Masallacin Qudus

Masu gadin Masallacin Qudus sun rusa wani makircin tsagerun Yahudawan Sahyoniyya na rusa yankin Babu-Rahmah na Masallacin Qudus.

Babban daraktan kula da Masallacin Qudus Umar Al-Kaswani ya bayyana cewa: Da jijjifin safiyar jiya Asabar wasu gungun tsagerun Yahudawan Sahayoniyya sun farma yankin Babu-Rahmah na Masallacin Qudus da nufin rusa shi, amma suka fuskanci maida martani daga masu gadin Masallacin lamarin da ya rusa bakar aniyarsu.

Al-Kaswani ya kara da cewa: Bayan samun nasarar korar tsagerun Yahudawan na Sahayoniyya, 'yan sandan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun gargadi masu gadin Masallacin tare da barazanar kama su.