Jul 09, 2018 06:42 UTC
  • 'Yan Gudun Hijra Dubu Goma Sun Koma Gida A Kudancin Siriya

Sama da 'yan gudun hijra dubu 10 ne suka koma gida bayan cimma yarjejjeniya tsagaita wuta a kudancin Siriya.

Kamfanin dillancin labaran Meher ya nakalto tashar Almanar na cewa masu rajin kare hakin bil-adama a Siriya sun sanar da cewa daga lokacin da rikici ya yi kamari tsakanin Sojojin Siriya da 'yan ta'adda a hanyoyin dake kai zuwa  iyakar kasar da Jodan sama da Mutane dubu 60 suka yi hijra a yankin, a yanzu ganin cewa an cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta kuma konciyar hankali ya dawo, muna tunani mafi yawa daga cikin mazauna yankin za su koma gidajensu.

A halin yanzu mafi yawan daga cikin yankunan kudancin kasar , musaman yankunan dake kewaye da birnin Dar'a na karkashin ikon gwamnatin Siriya ne, da hakan ya bawa 'yan gudun hijra da yawa komawa gidajensu.

A ranar juma'ar da ta gabata, gwamnatin Siriya ta bayyana cewa wasu kungiyoyin dake dauke da makamai na kasar sun cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta da gwamnatin Rasha,inda suka amince su meka makamansu ga dakarun tsaron kasar ta Siriya

Tags