Jihadul-Islami Ta Mai Da Martani Akan Killace Yankin Gaza
(last modified Tue, 10 Jul 2018 12:29:03 GMT )
Jul 10, 2018 12:29 UTC
  • Jihadul-Islami Ta Mai Da Martani Akan Killace Yankin Gaza

Kungiyar gwagwarmayar ta Paladinawa ta ce; Rufe iyakokin shiga yankin Gaza da 'yan sahayoniya su ka yi daidai yake da shelanta yaki akan al'ummar Gaza.

A jiya litinin ne dai haramtacciyar Kasar Isra'ila ta rufe masigar Karam Abu Salim da yake a matsayin babbar hanyar shiga da ficen kayan masarufi da zuwa yankin Gaza.

Kungiyar ta Jihadul-Islami ta ci gaba da cewa; ci gaba da takurawa al'umma Gaza da killace su ba zai sa su yin rauni ba balle su ja da baya akan tafarkin gwagwarmaya domin kare hakkokinsu.

Bayanin na kungiyar Jihadul-Islami ya kuma ce; Wannan irin siyasar ta nuna wariya da haramtacciyar kasar Isra'ila take aiki da ita, babu inda za ta kai ta balle ya yi tasiri.

Tun a 2006 ne dai haramtacciyar Kasar isra'ila ta killace yankin na Gaza da hana kai da komowar muhimman kayan da ake bukatuwa da su.