Ivory Coast : Jirgin Sama Na Soja Mallakin Faransa Ya Fadi
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32287-ivory_coast_jirgin_sama_na_soja_mallakin_faransa_ya_fadi
Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; Jirgin saman mai saukar angulu na soja ya fado ne a wani wuri mai nisan kilo mita 20 daga birnin Abidjan
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Jul 12, 2018 06:34 UTC
  • Ivory Coast : Jirgin Sama Na Soja Mallakin Faransa Ya Fadi

Kamfanin dillancin labarun Reuters ya nakalto cewa; Jirgin saman mai saukar angulu na soja ya fado ne a wani wuri mai nisan kilo mita 20 daga birnin Abidjan

Rahoton ya ci gaba da cewa mutum guda ya mutu yayin da wani kuma ya jikkata.

Sojojin Faransa a kasar sun ce jirgin ya fado ne a lokacin d ayake kai gudanar da wani shawagi na aiki. Tuni an dauki wanda ya jikkatan zuwa kasar Faransa domin samun magani.

Faransa ta girke sojojinta a cikin kasashe da dama na Afirka tun daga 2013 da sunan fada da ta'addanci. A cikin kasashen Mali da Afirka ta tsakiya da jamhuriyar Nijar kasar ta Faransa tana da sansanonin soja.