An Hallaka Wani Sojin Isra'ila A Gaza
Rundinar sojin yahudawan mamaya na Isra'ila ta ce, an kashe wani sojinta guda a kusa da zirin Gaza, wanda shi ne karon farko tun bayan yakin 2014.
A sanarwar data fitar rundinar ta ce, lamarin ya auke ne bayan da aka harbin sojojin inda daya daga cikinsu ya mutu sakamakon raunukan da ya samu.
Kafin hakan dama an rawaito shahadar wasu Palasdinawa hudu da sojojin yahudawan suka kashe a jiya Juma'a.
Tun ranar 30 ga watan Maris ne Palasdinawa ke zanga zangar a yankin, domin nuna fishinsu akan matakan da yahudawan sahayoniya ke dauka a zirin Gaza da kuma bukatar komawar 'yan gudun hijira Palasdinun da aka kora ko kuma suka kaurace wa muhallansu bayan kirkiro Israila a shekara 1948 komawa gida.
Kawo yanzu dai Palasdinawa 149 ne sojojin Isra'ila suka kashe, kana wasu sama da 4,000 suka raunana sakamakon harbin bindiga.