MDD Ta Yi Gargadin Akan Halin Da Mutane Gaza Suke Ciki
(last modified Tue, 24 Jul 2018 12:35:59 GMT )
Jul 24, 2018 12:35 UTC
  • MDD Ta Yi Gargadin Akan Halin Da Mutane Gaza Suke Ciki

Kwamishinan Kare Hakkin Dan'adam na MDD ne ya yi gargadin cewa halin da ake ciki a Gaza ya yi muni matuka

Zeid Ra'ad Al-Hussein da ya gabatar da jawabi a wurin taron kwamitin kare hakkin al'ummar Palasdinu a cibiyar Majalisar Dinkin Duniya dake birnin Newyork ya ce; An sami tsanantar yanayi a Gaza saboda rashin kudi mai tsanani da kungiyoyin agaji suke fama da shi ta yadda ba za su iya taimakawa 'yan gudun hijira ba.

Amurka ta janye kudaden da suka kai dala miliyan 65 da take bai wa hukumar da ke kula da 'yan gudun hijirar Palasdinawa (UNRUWA) bisa dalilin cewa sai  an sake wa kungiyar fasali.

Har ila yau Al Hussain ya yi tir da dokar wariya da aka yi a majalisar Knesett akan cewa; Yahudawa ne kadai 'yan kasa sannan ya ce: Abu ne mai yiyuwa yanayin da Gaza ke ciki zai kara tsananta.