Jihadul-Islami Ta Gargadi Haramtacciyar Kasar Isra'ila
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i32485-jihadul_islami_ta_gargadi_haramtacciyar_kasar_isra'ila
A wani bayani da reshen soja na kungiyar Jihadul-Islami ya fitar a jiya Laraba ya ce; Duk wata ta'asa da 'yan sahayoniya za su tafka akan al'ummar Palasdinu za su fuskanci mayar da martani
(last modified 2018-08-22T11:32:09+00:00 )
Jul 26, 2018 06:59 UTC
  • Jihadul-Islami Ta Gargadi Haramtacciyar Kasar Isra'ila

A wani bayani da reshen soja na kungiyar Jihadul-Islami ya fitar a jiya Laraba ya ce; Duk wata ta'asa da 'yan sahayoniya za su tafka akan al'ummar Palasdinu za su fuskanci mayar da martani

Bayanin ya ci gaba da cewa; rundunar masu jihadi za ta kare jinin al'ummar palasdinu da yan sahayoniyar suke shekarwa.

Wannan bayanin ya zo ne a daidai lokacin da sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra'ila suke ci gaba da kai hare-hare da manyan bindigogi akan gabacin zirin Gaza. A kalla palasdinawa 4 ne aka tabbatar da sun yi shahada, yayin da wasu masu yawan gaske su ka jikkata.

Kai wa yankin Gaza hare-hare da manyan bindigogi da 'yan sahayoniya suke yi ya zama ruwan dare tun daga 2017. A tsawon wannan lokacin palasdinawa masu yawa sun yi shahada da kuma jikkata.