Yawan 'Yan Jaridun Da Jami'an Tsaron Isra'ila Suka Kama Ya Karu
A jiya Litinin Dakarun tsaron Haramtacciyar kasar Isra'ila sun kame Ibrahim Arratisi dan jaridar TRT na kasar Turkiya a yankin kogin jodan
Kamfanin dillancin labaran Qudus Qudusuna yahabarta cewa bayan kamun da aka yiwa Ibrahim Arratisi a Palastinu, adadin 'yan jaridun da jami'an tsaron Isra'ila suka kame ya haura zuwa shiga cikin mako guda kacal.
A cikin watanin baya-bayan nan yahudawan sahayuwa sun tsananta kame-kamen 'yan jaridu a yankin Palastinu.
A bangare guda, yahudawan sahayunan sun hana wata tawagar kasar Turkiya shiga garin Qudus, inda tun daga filin saukar jiragen sama ta mayar da su kasarsu.
Radion Sahayuna ta sanar da cewa jami'an filin jirgin saman kasa da kasa na Ben Gurion sun mayar da tawagar turkiya mai dauke da mutane 90 kasarsu, wasu daga ciki ma saida aka yi musu tambayoyi kafin a mayar da su kasar su.
Wannan lamari dai na zuwa ne bayan zargin juna tsakanin shugaba Erdugan na Turkiya da Piraministan Isra'ila Benjamine Natanyahu, bayan da Shugaba Erdogan ya zarki wasu daga cikin hukumomin Isra'ilan da kama karya bayan amincewa da dokar wariya da Majalisar HK Isra'ilan ta amince da ita.