Masar: Kungiyar Ikhwanul Muslimin Ta Bukaci A Gudanar Da Zaben Gaggawa
(last modified Wed, 15 Aug 2018 12:52:11 GMT )
Aug 15, 2018 12:52 UTC
  • Masar: Kungiyar Ikhwanul Muslimin Ta Bukaci A Gudanar Da Zaben Gaggawa

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya yi wannan kiran ne a daidai lokacin da ake cika shekaru biyar da tarwatsa gangamin Rabi'a al-adawiya da jami'an tsaron kasar su ka yi

Sanarwar ta 'yan'uwa musulmi ta bukaci shugaban kasa Abdul fattaha al-Sisi da ya gudanar da zaben gaggawa domin kawo karshen takaddamar siyasa a kasar.

Sanarwar ta kuma soki  gwamnatin Abdulfattah al-sisy da amfani da karfi wajen murkushe 'yan adawar siyasa, don haka yin zaben gaggawa shi ne hanyar kawo karshen dambaruwar siyasar kasar.

Masar ta fada cikin dambaruwar siyasa a 2013 da aka kifar da gwamnatin Muhammadu Mursi na kungiyar 'yan'uwa musulm.