Adadin Palasdinawa Da Su Ka Yi Shahada Ya Karu
(last modified Sat, 15 Sep 2018 09:26:14 GMT )
Sep 15, 2018 09:26 UTC
  • Adadin Palasdinawa Da Su Ka Yi Shahada Ya Karu

Masu Zanga-zangar hakkin komawa kasarsu ta gado, sun fusanci kai hare-hare daga sojojin Sahayoniya.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Palasdinu ta sanar da cewa; Mutane uku ne su ka yi shahada a yayin gangamin na Palasdinawa a yankun zirin Gaza daga cikin hadda wasni matashi dan shekaru 14, yayin da wasu mutane 3o su ka jikkkata.

Tun da fari an sanar da shahadar mutane biyu ne a tsakanin palasdinawan da suke gangami a kan iyaka da zirin Gaza da yankuna da suke ci gaba da zama a karkashin 'yan mamaya.

Wannan shi ne karo na 25 da Palasdinawan su ke yin gangami a kusa da iyaka da Gaza domin tabbatar da hakkinsu na komawa gidajensu da aka kore su daga ciki yayin kirkirar haramtacciyar kasar Isra'ial.

An fara gudanar da Zanga-zangar ne dai tun a ranar 30 ga watan Maris wadda kuma take ci gaba a duk ranar juma'a.