Harin Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ya Yi Sanadiyyar Shahadar Bapalasdine Guda
(last modified Mon, 24 Sep 2018 06:51:00 GMT )
Sep 24, 2018 06:51 UTC
  • Harin Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra'ila Ya Yi Sanadiyyar Shahadar Bapalasdine Guda

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan yankin Zirin Gaza, inda suka janyo shahadar bapalasdine guda tare da jikkatan wasu adadi masu yawa.

Ma'aikatar lafiya ta Palasdinu a yammacin jiya Lahadi ta sanar da cewa: Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan yankin gabashin Zirin Gaza lamarin da ya yi sanadiyyar shahadar bapalasdine guda tare da jikkatan wasu goma sha hudu na daban.

Har ila yau kakakin ma'aikatar lafiya a Palasdinu Ashraf Al-Qudurah ya sanar da cewa: Tun bayan bullar zanga-zangar lumana domin jaddada hakkin Palasdinawa 'yan gudun hijira na dawowa kasarsu ta gado a watan Maris na wannan shekara zuwa yanzu, Palasdinawa 184 ne suka yi shahada sakamakon hare-haren ta'addancin sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila kansu.