Sharhi: Taron Arba'een Na Imam Hussain (AS) A Karbala Iraki
(last modified Wed, 31 Oct 2018 05:47:06 GMT )
Oct 31, 2018 05:47 UTC
  • Sharhi: Taron Arba'een Na Imam Hussain (AS) A Karbala Iraki

A jiya Talata ce aka gudanar da taron arbaeen na shahadar Imam Hussain (AS) a birnin karbala na kasar Iraki, tare da halartar miliyoyin mutane daga ciki da wajen kasar ta Iraki.

Taron arbaeen wanda ake gudanar da shi a kowace rana ta 20 ga watan safar, a halin yanzu shi ne taro mafi girma a duniya da yake hada miliyoyin mutane wuri guda.

Hukumomin kasar Iraki sun sanar da cewa, fiye da mutane miliyan 14 ne suka halarci taron na arbaeen da ya gudana a jiya a hubbaren Imam Hussain (AS) da ke cikin birnin Karbala a kudancin kasar ta Iraki, kusan miliyan 3 daga cikin masu ziyarar sun fito daga kasashen duniya 43, sauran fiye da miliyan 11 kuma sun fito ne daga sassa na kasar Iraki.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa, kafofin yada labarai kimanin 400 da kuma 'yan jarida kimanin 600 daga kasashen duniya daban-daban ne suka halarci wurin domin bayar da rahotani a kan taron.

Ta fuskacin tsaro kuwa, mahukuntan Iraki sun ce tun makonni kafin lokacin gudanar da tarukan na arbaeen ne aka fara daukar kwararan matakan tsaro a dukkanin yankunan da masu tattaki suke bi zuwa birnin Karbala, kamar yadda kuma aka dauki irin wadannan matakai a ciki da wajen birnin tun a cikin makonnin da suka gabata, inda jami'an tsaro fiye da dubu 30 suka gudanar da ayyukan tabbatar da tsaro a yayin wannan babban taro.

Bayanin ya kara da cewa, sakamakon irin wadannan kwararan matakan tsaro da aka dauka, an samu nasarar gudanar da taron ba tare da samun hare-haren ta'addanci ba, duk kuwa da cewa an cafke wasu daga cikin 'yan ta'adda da suka shige cikin masu tattaki, da nufin aiwatar da ayyukan ta'addanci, daga cikinsu har da wadanda suka yi shigar mata, amma duk da haka jami'an tsaro sun gano su, kuma sun kame su.

Taron na arbaeen a wannan shekara ya samu halartar wakilan wasu kungiyoyin na kasashen ketare da suka hada da na kare hakkokin bil adama, musamman ma daga kasashen Amurka, Birtaniya Canada Australia da sauransu, wadanda suke kallon kisan Imam Hussain (AS) babban zalunci ne da aka aikata  akan 'yan adamtaka a tarihi, duk da cewa da dama daga cikinsu ma ba musulmi ba ne, amma suna kallon cewa Imam Hussain (AS) wani mutum ne ya kamata a jinjina masa saboda sadaukarwar da ya yi domin takawa zalunci da azzalumai birki, da kuma kare akidar da ya yi imani da ita ta addininsa daga yunkurin masu neman gurbata wannan akida.

Ko shakka babu, sadaukantarwar Imam Hussain (AS) tana a matsayin wani babban darasi ne da al'ummomin duniya suke dauka wajen dagewa  a kan bin gaskiya da kuma sadaukarwa domin wanzuwarta, da kuma 'yantar da kai daga danniyar masu girman kai, kamar yadda tsohon Firayi ministan kasar India wanda ya yi gwagwarmaya da turawan mulkin mallaka a kasar Mahatima Ghandi ya tabbatar da hakan, inda ya ce, ya dauki darasi daga juriya irin ta Imam Hussain, wajen fuskantar zalunci da danniya ta 'yan mulkin mallakar Birtania a kan al'ummar kasar India.