An Samu Dan Sukuni A Ranar Juma'a A Zirin Gaza
(last modified Sat, 03 Nov 2018 06:30:01 GMT )
Nov 03, 2018 06:30 UTC
  • An Samu Dan Sukuni A Ranar Juma'a A Zirin Gaza

Karon farko cikin 'yan watanni an samu ranar Juma'a da aka samu dan sukuni a yankin zirin Gaza, bayan shafe dogon lokaci na arangama tsakanain Palasdinawa dake neman 'yancinsu da kuma sojojin yahudawan mamaya na Isra'ila.

Hakan dai ya biyo bayan da Masar ta shiga wata tattaunawa ta tsakanin mahukuntan yahudawan da kuma kungiyar gwagwarmaya musulinci ta Hamas. 

Bayanai sun nuna cewa Masar ta samu cimma wata yarjejeniya, data tanadi kungiyar ta Hamas data kawo karshen zanga-zangar a iyaka da Isra'ilar, a yayin da su kuwa mahukuntan yahudawan zasu sassauta jerin matakan tsawan shekaru goma da suka dauka a yankin na zirin Gaza.

Ma'aikatar kiwan lafiya ta Hamas  ta ce Palasdinawa 7 ne suka jikkata a yayin harbin sojojin Isra'ilar, alkalumman da suka kasance mafi karamci idan aka kwatantan da sauren ranakun Juma'a da suka gabata.

Saidai har kawo yanzu babu wani bayyani a hukumance daga bangarorin da batun ya shafa a yarjejeniyar da Masar ke shiga tsakani, amma kafofin yada labaren isra'ila sun ce matakin ya tanadi yadda Qatar zata shigar da man fetur domin samar da wutar lantarki a Gaza da kuma biyan albashin ma'aikatan da kungiyar Hamas ta aza, ta yadda za'a samu zaman lafiya a yankin.