Adadin Falastinawa Da Suka Shahada A Wannan Shekara Ya Kai 316
(last modified Sat, 03 Nov 2018 19:13:12 GMT )
Nov 03, 2018 19:13 UTC
  • Adadin Falastinawa Da Suka Shahada A Wannan Shekara Ya Kai 316

Majiyoyin gwamnatin Palastine sun ce; tun daga lokacin da Trump ya shelanta birnin Qods a matsayin babban birnin Isra’ila ya zuwa yanzu Falastinawa 316 ne suka yi shahada.

Kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, kwamitin da ke bin kadun lamarin Falastinawa da suka yi shahada ya bayar da bayanin cewa, daga lokacin da Trump ya dauke ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Qods a matsayin babban birnin Isra’ila ya zuwa yanzu Falastinawa 316 ne suka yi shahada sakamakon bude wutar da sojojin Isra'ila ke yia  kansu, daga ciki har har da kananan yara 68 da kuma ‘yan gwagwarmaya 19.

Bayanin ya ce kimanin 204 daga cikin wadanda suka yi shahada daga yankin zirin Gaza suke, yayin da sauran kuma daga yankunan Quds da gabar yamma da kogin Jordan da sauransu.

A ranar 6 ga watan Disamban 2016 ne dai shugaban Amurka ya shelata dauke ofishin jakadancin Amurka daga birnin Tel aviv zuwa Qods, lamarin da ya fuskanci adawa daga kasashen duniya, kuma tun daga lokacin Falastinawa suna ci gaba da bijirewa wannan kudiri.