Gwamnatin Masar Ta Jaddada Goyon Bayanta Ga Shirin Kafa Kasar Palasdinu
Shugaban kasar Masar ya jaddada matsayin gwamnatin kasarsa na goyon bayan kafa yantacciyar kasar Palasdinu mai cin cikakken gashin kai kuma gabashin Qudus ya zame babban birnin kasar.
A ganawarsa da shugaban hukumar cin kwarya-kwaryar gashin kan Palasdinawa Mahmud Abbas a tsibirin Sharmus-Sheikh na Masar a jiya Asabar: Shugaban kasar ta Masar Abdul-Fatah Al-Sisi ya bayyana cikakken goyon bayansa ga shirin kafa yantacciyar kasar Palasdinu mai cin cikakken gashin kai a kan iyakar da aka shata a shekara ta 1967 kuma yankin gabashin Qudus ya zame babban birnin kasar.
A nashi bangaren shugaban hukumar Palasdinawa Mahmud Abbas ya bayyana irin kokarin da hukumarsa ke yi na ganin an samu hadin kai a tsakanin al'ummar Palasdinu musamman a tsakanin kungiyoyin Palasdinawa.
Har ila yau shugabannin biyu sun tattauna batutuwan da suka shafi alakar da ke tsakanin Masar da Palasdinu da matsalolin da suke ci gaba da addabar yankin gabas ta tsakiya da ma duniya baki daya.