Iran : Za Mu Karya Laggon Takunkuman Amurka
(last modified Mon, 05 Nov 2018 11:15:46 GMT )
Nov 05, 2018 11:15 UTC
  • Iran : Za Mu Karya Laggon Takunkuman Amurka

Shugaba Hassan Rohani na Jamhuriyar Musulinci ta Iran, ya yi alkawarin cewa kasarsa zata karya laggon jerin takunkuman da Amurka ta sake kakaba mata.

Yau Litini ne Amurka zata sanar da sake dawo da dukkan takunkumanta wanda ta danganta da mafi tsanani da ba'a taba kakaba wa wata kasa ba ga Iran.

Takunkuman zasu shafi bangaren makamashi da kuma harkokin bankuna, saidai a cewar Shugaban kasar ta Iran Dakta Rohani, kasarsa zata duk abunda zatayi na kewaye takunkuman zaluncin na Amurka da suka sabawa dokokin kasa da kasa.