Matakin Isra'ila Na Hana Palastinawa Gudanar Da Zanga-Zanga
Bayan Shahadar matashin bapalastine a hanun sojojin sahayuna, adadin shahidan na zanga-zangar lumana da Palastina ke yi na neman dawo da hakin kasarsu ya haura zuwa 233.
Bayan kwashe kimanin kwanaki 200 da palastinawa ke gudanar da zanga-zangar lumana na dawo da hakin kasarsu, wanda suka fara tun daga ranar 30 ga watan Maris na wannan shekara da muke ciki, hukumomin Isra'ila suna amfani da karfin da ya fice gima na hana Palastinawan zanga-zanga, inda aka kiyasta cewa cikin ko wani wata Palastinawa 35 ne ke shahada ta hanyar harsashen Sojojin Sahayuna.
Cibiyar sadarwar Palastinu ta ce daga cikin shahidai 233, 43 kananen yara ne, 5 kuma mata, sai jami'an agajin gaggauwa guda uku, sannan akwai 'yan jarida guda biyu, ko baya ga wadanda suka yi shahadar akwai mutune dubu 43 da suka jikkata.
Yawan wannan kisa na ta'addanci da sahayunan ke yiwa Palastinawan shike nuna cewa mahukuntan Isra'ilan nada fargaba a game da zanga-zangar neman dawo da hakin kasarsu, to amma minene dalilin wannan fargabar? da farko wannan zanga-zanga na gudana ne ko wani mako, sannan kuma Palastinawan na gudanar da zanga-zangar ne bisa imani da akidar kare kasarsu ta haifuwa da addininsu, tare kuma da rusa duk wani shiri na Isra'ila da Amurka na canza yanayin yankin.
Wannan Shirin karni da Amurka ta gabatar a aikate ya raba duban Palastinawa daga gidajensu da kuma kasarsu da haifuwa, kuma a bangare guda ya yi sanadiyar mamaye wani bangare mai yawa na yankin Palastinu musaman ma birnin Qudus da yake a matsayin Alkibilar farko na al'ummar musulmi, wannan kuma shi ne ya sanya al'ummar Palastinun ta dauki kudirin gudanar da zanga-zangar lumana na dawo da hakin kasarsu, da kuma suka fara tun a ranar 30 ga watan Maris har lokacin da samu nasara a kan hukumomin sahayunan.
Ama a maimakon, Duniya musaman kasashen musulmi da na Laraba su goya musu baya a wannan yaki da suke yi, wasu shugabanin kasashen Larabawan ma kamar su Saudiya, hadaddiyar daular Larabawa, da Bahren gami da Oman a baya-bayan na kokarin dawo da alakarsu da haramtacciyar kasar Isra'ila.