Hamas Ta Yi Wa Isra'ila Ruwan Rokoki Fiye Da 200
Kungiyar Hamas ta kai hare haren rokoki fiye da 200 a matsayin maida martani ga Isra'ila, kan kashe wasu Falasdinawa bakwai, ciki har da wani kwamandan kungiyar ta Hamas.
Majiyoyin Falasdinawa sun ce lamarin ya auku ne bayan da wasu sojojin mamaya na Isra'la da ke tafiya a motar fararen hula suka tsallaka zirin Gaza, a yayin da aka gano su a wajen wani binciken abubuwan hawa.
A nan ne kuma Yahudawan suka bude wuta, suka kashe kwamandan na hamas Nur Barakeh.
Wasu rahotanni na daban sun tabbatar da kashe wani kwamandan sojojin mamaya na 'yan sahayoniya.
Lamarin dai ya sake tayar da wani rikici a tsakanin yahudawan mamayar na Isra'ila da Falasdinawan yankin zirin Gaza, inda Isra'ila ta kai hare-hare ta sama, kan abunda ta kira farmaki kan kadarorin kungiyar Hamas da ta Islamic Jihad, wanda ya kai ga shahadar Falasdinawa uku.