Palasdinawa Biyu Sun Yi Shahada Sanadiyar Hare-Haren HKI
Palasdinawa biyu ne suka yi shahada a lokacinda sojojin HKI suka kai hare-hare kan yankin Gaza na kasar Palasdinu da aka mamaye a yau Talata
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ashraf Al-qidra kakakin ma'aikatar lafiya na yankin Gaza yana fadar haka a yau Talata. Ya kuma kara da cewa wasu da dama sun ji rauni a lokacin sojojin yahudawan suka kai hare hare a kan wani yanki da ake kira Salati yamma da garin Bait-Lahia mai tazarar kilomita 5 daga garin gaza.
Banda haka Ashraf ya kara da cewa wani matashi dan shekara 20 mai suna Mus'ab Hus ya yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni a wani harin da sojojin yahudawan suka kai a unguwar Zaitun na yankin gaza.
Kafin haka dai kungiyar Hamas ta yi ruwan makamai masu linzami a kan kudancin yankunan da yahudawa suka mamaye da su, wanda ya halaka yahudawa da dama ya kuma tilastawa gwamnati yahudun amincewa da tsagaita bude wuta.