Makaman Kariya Na Siriya Sun Maida Martani Kan Hare-haren Israi'la
(last modified Fri, 30 Nov 2018 04:43:48 GMT )
Nov 30, 2018 04:43 UTC
  • Makaman Kariya Na Siriya Sun Maida Martani Kan Hare-haren Israi'la

Makaman garkuwa na kare sararin samaniyar Siriya sun maida martani tare da kakkabo makamai masu linzami da jiragen sojin Isra'ila suka harba a kudancin birnin Damascos da kuma kudancin kasar.

Sanarwar da rundinar kare sararin samaniyar Siriya ta fitar, ta ce makamn garkuwanta sunyi nasara dakile harin jiragen sama na makiya a lardinan Keswa da Harfa a kusa da tuddan Golan, a cikin daren jiya Alhamis.

Wata majiyar tsaro Siriya ta shaidawa masu aiko da rahotanni cewa an harbo makamai masu linzamin da dama da  jiragen na Isra'ilar suka harbo, kuma duk hare haren da aka kai basu cimma manufarsu ba.

Wannan dai shi ne karo na farko da jiragen yahudawan mamaya na Isra'ilar suka kai tun bayan na ranar 16 ga watan Satumba, lokacin da makaman kare sararrin samaniyar na Siriya suka harbo wani jirgin sojin Rasha, wanda Rasha ta dora alhakin hakan ga Isra'ilar.

Bayan hakan ne kuma a farkon watan Oktoba da ya gabata, kasar ta Rasha ta sanar da mika wa Siriya makaman garkuwa kan hare haren sama na S-300.