Kasar Qatar Ta Bayyana Kungiyar Larabawan Tekun Pasha Da Gajiyawa
Ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhammad Bin Abdurrahman Ali-Thany ne ya bayyana cewa; A zahiri kungiyar tana nan,amma a aikace ba ta aiwatar da komai
Ministan harkokin wajen na kasar Katar wanda yake gabatar da jawabi a wurin taron kasa da kasa a birnin Doha, ya ci gaba da cewa; Kungiyar ta kasashen larabawan yankin takun pasha tana da bukatar a yi mata kwaskwarima saboda a halin yanzu ita da babban magatakardanta ba su da wani zabi a hannunsu
Tun da fari, sarkin kasar ta Katar wanda ta bude taron da jawabi ya yi ishara da killace kasarsa da kasashen Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Bahrain su ka yi, sannan ya kara da cewa; Matsayar kasar Katar ba ta sauya ba, kuma a kodayaushe tana yin kira a nisanci tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe
Jigron taron kasa da kasa na Doha ya mayar da hankali ne akan tattauna siyasar kasashe a cikin duniyar da take cudanya da juna
Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a wurin taron na kwanaki biyu da akwai babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya da kuma Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad Zarif