Za'a Rage Yawan Tallafin Abinci Da Ake Bawa Palasdinawa
(last modified Wed, 19 Dec 2018 18:57:01 GMT )
Dec 19, 2018 18:57 UTC
  • Za'a Rage Yawan Tallafin Abinci Da Ake Bawa Palasdinawa

Hukumar abinci ta duniya wato World Food Programme (WFP) ta bada sanarwan cewa zata rage yawan abincin da take tallafawa Palasdinawa da shi a sabon shekara ta 2019.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya ce hukumar ta abinci ta duniya ta bada wannan sanarwan ne a yau Laraba ta kuma kara da cewa ta dauki wannan matakin ne don karancin kudaden da take fama da shi.

labarin ya kara da cewa mutane kimani dubu 27 ne ba zasu sami tallafin da suka saba samu a yankin yamma da kogin Jordan, sannan  a yankin gaza kuma zata rage tallafi na kashi 20% da take kaiwa yankin.

A cikin watan Augustan shekarar da muke ciki ne gwamnatin kasar Amurka ta dakatar da tallafin dalar Amurka miliyon 200 da take bawa yankin Gaza, sannan ta dakatar da tallafin dalar Amurka miliyon 360 da take bawa Palasdinawa a ko wace shekara ta hukumar UNARWA.

An kafa hukumar UNARWA ne a shekara 1949 don tallafawa Palasdinawa yan gudun hijira da suke kasashen Jordan, Siriya, Lebanon da kuma yankin yamma da kogin jordan da kuma Gazza.