"Yan Gudun Hijirar Syria Sun Koma Garin Minbaj
Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ce 'yan gudun hijira masu yawa ne su ka tsallaka mashigar Tayhah zuwa garin Minbaj da ke gundumar Halab
Jami'an gwamnatin Syria sun sanar da cewa an cimma yarjejeniyar a tsakanin mayakan Kurdawa a jiya Laraba domin janye sojojinsu zuwa baya
Sojojin Syria sun shiga cikin garin na Minbaj ne da kuma ficewar sojojin Kurdawa bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa kasarsa za ta janye sojojinta daga cikin kasar ta Syria
Amurkan tana da sojoji 2000 a cikin kasar Syria
Wani labarin daga kasar Syria ya ce; Mutanen garin Hasakah sun yi Zanga-zangar nuna kin amincewa da barazanar da Turkiya take yi na aikewa da sojojinta domin murkushe kungiyoyin Kurdawa
A cikin shekaru biyu na bayan nan Turkiya ta rika kai hare-hare akan Kurdawa a cikin garuruwan al-Bab, Jarablus, da Ifrin da suke a arewacin kasar ta Syria