"Yan Gudun Hijirar Syria Sun Koma Garin Minbaj
(last modified Thu, 03 Jan 2019 19:06:07 GMT )
Jan 03, 2019 19:06 UTC

Rahotannin da suke fitowa daga Syria sun ce 'yan gudun hijira masu yawa ne su ka tsallaka mashigar Tayhah zuwa garin Minbaj da ke gundumar Halab

Jami'an gwamnatin Syria sun sanar da cewa an cimma yarjejeniyar a tsakanin mayakan Kurdawa a jiya Laraba domin janye sojojinsu zuwa baya

Sojojin Syria sun shiga cikin garin na Minbaj ne da kuma ficewar sojojin Kurdawa bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa kasarsa za ta janye sojojinta daga cikin kasar ta Syria

Amurkan tana da sojoji 2000 a cikin kasar Syria

Wani labarin daga kasar Syria ya ce; Mutanen garin Hasakah sun yi Zanga-zangar nuna kin amincewa da barazanar da Turkiya take yi na aikewa da sojojinta domin murkushe kungiyoyin Kurdawa

A cikin shekaru biyu na bayan nan  Turkiya ta rika kai hare-hare akan Kurdawa a cikin garuruwan al-Bab, Jarablus, da Ifrin da suke a arewacin kasar ta Syria