Ziyarar Pompeo Zuwa Kasashen Gabas Ta Tsakiya Bata Cimma Nasara Ba.
Ziyarar da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo yake yi a wasu kasashen gabas ta tsakiya ba zasu kai ga manufar Amurka na wannan ziyarar ba.
Tashar talabijin ta Al-Hadath ce ta bayyana haka a jiya Alhamis ta kuma kara da cewa a ziyararsa ta farko a yankin a kasar Masar Pompeo ya bayyana damuwar gwamnatin kasar Amurka da yadda kasar Iran ta sami karbuwa a wasu kasashen yankin.
A wani jawabin hadin guiwa wanda Mike Pompeo da kuma tokoransa na kasar Masar Sameh Shukri suka gudanar, ministan harkokin waje na kasar Masar ya bayyana cewa sun tattauna batun rikicin gabas ta tsakiya da kuma matsalolin yankin.
Sannan a nashi bangaren Pompeo ya ce gwamnatinsa zata fice daga kasar Siriya kamar yadda shugaban Donal Trump ya bayyana amma kuma ya nuna damuwarsa da yadda kasar Iran tayi kakagiga a kasar Siriya.
A farkon makon da yake karewa ne sakataren harkokin waje na kasar ta Amurka ya fara ziyara na kwanaki 7 zuwa kasashe 8 na yankin gabas ta tsakiya.
Gwamnatin kasar Amurka tana bawa kasar Masar dalar Amurla billiyon guda da million 300 a ko wace shekara tun bayan ta rattaba hannun kan yerjejeniyar camp Devid da HKI a shekara 1979