An Wanke Shugabannin Kungiyar Ikhwanul Mislimin Da Dama A Masar
(last modified Fri, 11 Jan 2019 06:40:00 GMT )
Jan 11, 2019 06:40 UTC
  • An Wanke Shugabannin Kungiyar Ikhwanul Mislimin Da Dama A Masar

Wata kotun daukaka kara a kasar Masar ta wanke wasu shuwagabannin kungiyar yan'uwa musulmi ta kasar daga dukkan laifuffuka da ake tuhumarsu.

Majiyar Muryar JMI ta bayyana cewa wata kotun daukaka kara a yankin Jiza kusa da birnin Alkahira babban birnin kasar ta wanke shuwagabannin kungiyar yan'uwa musulmi 8 daga ciki har da shugaban Kungiya Mohammad Badie daga dukkan laifuffukan da ake tuhumarsu da su. 

Labarin ya kara da cewa kotun ta wanke shuwagabannin wannan kungiyar daha laifuffuka wadanda suka hada da kisan kai, shiga kungiyar da aka haramta, lalata harkokin tsaron kasa, lalata dokiyoyin jama'a da kuma lalata dukiyoyin wasu mutane.

Wannan shi ne karon farko da wata kotu ta wanke shugabannin wannan kungiyar tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaban Mohammad Mursi jiyin mulki a shekara ta 2013.