Dakarun HKI na ci gaba da rusa gidajen Palastinawa
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3484-dakarun_hki_na_ci_gaba_da_rusa_gidajen_palastinawa
Dakarun tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila na ci gaba da rusa gidajen Palastinawa
(last modified 2018-08-22T11:28:05+00:00 )
Apr 06, 2016 09:56 UTC
  • Dakarun HKI na ci gaba da rusa gidajen Palastinawa

Dakarun tsaron Haramcecciyar kasar Isra'ila na ci gaba da rusa gidajen Palastinawa

Tashar telbijin din Al-Aksa ta habarta cewa a safiyar yau Laraba, manyan motocin rusa gidaje na Haramcecciyar kasar Isra'ila sun rusa gidan wani Bapaltine a garin Rahat na yankin Nakab dake gudancin Palastinu, baya ga haka, Dakarun HKI sun hana Palastinawa ko wani irin gini a yankin Nakab.

A Baitu Sahur dake jihar baitu Laham,manyan motocin rusa gidaje na HKI sun rusa wani bangare na gidan Bapaltine, har ila yau a garin Alkhalil dake gabar tekun Jodan sun yi galgadin rusa gidajen Palastinawa 12 saboda a cewar su kafin a gina gidajen, ba a karbi takardar bayar da izinin ginasu ba.

Sa'ib Arikan babban saktaren gine-gine na yankin Palastinu ya yi alawadai da wannan aika-aikan da magabatan HKI ke yi tare neman hukunta su a kotun hukunta manya laifuka ta kasa da kasa.