Jan 19, 2019 12:40 UTC
  • Amurka Na Shirin Yanke Taimakon Da Take Baiwa Falastinawa

Gwamnatin kasar Amurka na shirin yanke dukkanin tamakon da take baiwa gwamnatin kwarya-kwaryan cin gishin kan Palastine.

Jaridar Jeruslam Post ta bayar da rahoton cewa, tsohon babban manzon Amurka ai kula da taimakon da Amurka take baiwa Falastinwa Dave Harden ya bayyana cewa, gwamnatin Trump na shirin yanke dukkanin taimakon da take baiwa gwamnatin palastine, ta hanyar cibiyar USAID.

Ya ce gwamnatin Amurka ta dauki wannan matakin ne sakamakon yadda gwamnatin Palstine mai kwarya-kwaryan cin gishin kai taki amincewa da sharuddan da Amurka ta gindaya mata kafin ci gaba da karbar wannan taimako, bayan amincewa da dokar yaki da ta'addanci a cikin shekara ta 2018.

Daga cikin sharuddan kuwa har da dakatar da taimaka ma iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hannun jami'an Isra'ila, masu gwagwarmaya ne ko ba ma gwagwarmaya ba, sharadin gwamnatin Palastine takia mincewa da shi.

 

 

 

Tags