Jami'an Tsaron Sahayuna Sun Kai Farmaki Masallacin Aksa
(last modified Mon, 04 Feb 2019 19:13:12 GMT )
Feb 04, 2019 19:13 UTC
  • Jami'an Tsaron Sahayuna Sun Kai Farmaki Masallacin Aksa

Dakarun tsaron Sahayuna sun sake kai farmaki masallacin Aksa tare keta alfarmar wannan wuri mai tsarki.

Tashar talabijin din Al-alam dake watsa shirye-shiryenta daga nan birnin Tehran ta nakalto Faras Addabas jami'in dake kula da harakokin watsa labarai na kungiyar Awkaf ta musulinci a yankin Palastinawa ya sanar da cewa a wannan Litinin 'yan sandar haramtacciyar kasar Isra'ila bisa jagorancin shugaban 'yan sandar Yoram halleph sun kai farmaki masallacin Aksa.

A yayin kai farmaki, jami'an tsaron 'yan sandar na Sahayuna sun goge duk wata alama ta musulinci da kiristanci tare da maye gurbinsa da alamar yahudanci.

A bangare guda kuma, mazauna yankuna sahayuna sun kai farmaki a wannan Litinin Masallacin Al-Mirah dake kauyen Der Dibwan na gabashin Ramullah tare da rubuta alamomi na kyamar baki a bisa bangon masallacin.

Har ila yau rahoton ya ce a yayin kai farmakin da yahudawan suka kai cikin masallacin na Al-Mirah sun yi watsi da duk wasu abubuwa masu amfani na cikin masallacin.

A cikin 'yan watanin nan yahudawa bisa goyon bayan jami'an tsaron sahayuna sun tsananta kai hare-hare a masallacin Aksa da wurare masu tsarki na Musulinci a yankuna da wuraren da suka mamaye na Palastinawa, wannan kuma na zuwa ne tun bayan da shugaba Trump na Amurka ya shelanta Baitul-Makdis a matsayin babban birnin haramtacciyar kasar Isra'ila.