Kungiyoyin Hamas Da Jihadul Islami Sun Yi Allawadai Da Harin Zahidan
Kungiyoyin gwagwarmayar Falastine Hamas da Jihadul Islami sun yi Allawadai da harin ta'addancin da aka kai kan jami'an tsaron Iran a garin Zahidan.
a Cikin bayanan da suka fitar a jiya, Hamas da Jihadul Islami sun bayyana harin na Zahidan da cewa wani aiki ne ta'addanci, wanda ke nufin gurgunta kasar ta Iran, sakamakon irin matsayar da ta dauka wajen kin mika kai manufofin 'yan mamaya.
Hamas ta ce babbar manufar kai ma jami'an tsaron Iran ita ce kara karfafa samuwar Amurka acikin yankin gabas ta tsakiya domin kare manufofin Isra'ila a kan al'ummar yankin, musamman al'ummar Palastine.
A daren Larabar da ta gabata ce dai wasu 'yan ta'adda masu dauke da akidar kafirta musulmi suka kai wa wata motar bas da ke dauke da jami'an tsaron Iran masu gadin iyakoki hari, inda 27 daga cikinsu suka rasa rayuwansu, wasu 13 kuma suka samu raunuka.