Somaliya: An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Sansanin Soja
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34873-somaliya_an_kai_harin_kunar_bakin_wake_a_sansanin_soja
Wata majiyar sojan Somaliya ce ta ba da labarin kai harin kunar bakin waje akan sansanin soja da yake a kudancin kasar
(last modified 2019-01-20T06:33:16+00:00 )
Jan 20, 2019 06:33 UTC
  • Somaliya: An Kai Harin Kunar Bakin Wake A Sansanin Soja

Wata majiyar sojan Somaliya ce ta ba da labarin kai harin kunar bakin waje akan sansanin soja da yake a kudancin kasar

Jami'in soja Somaliya Ahmad Farah ya fadawa kamfanin dillancin labarun Anatoli na Turkiya cewa; Dan Kunar bakin waken da ya makare mota da bama-bamai ya kai hari akan sansnain Barisnagoni a gundumar Jubayi Suflah.

Jami'in sojan ya kara da cewa; Bayan harin an kuma yi taho mu gama mai tsanani a tsakanin sojoji da maharan kungiyar al-Shabab wanda ya dauki fiye da sa'a daya ana bugawa

Kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabab ta dauki nauyin kai harin.

An kafa sansanin sojan na garin Barisnagoni ne domin shirya kai farmakin soja akan tungar 'yan kungiyar al-Shabab da ke garin Bu'ali a gundumar Jubayi markazi.

Kungiyar al-Shabab tana a matsayin babbar barazanar tsaro ga kasar Somaliya da kuma makwabtanta