Feb 23, 2019 06:57 UTC
  • Jami'an Tsaron Yahudawa Sun Yi Awon Gaba Da Falastinawa Da Dama

Jami’an tsaron Isra’ila sun kame Falastinawa a yankuna daban-daban da ke kusa da birnin Quds a yau.

Shafin yada labaran arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, a jiya Juma'a jami’an tsaron Isra’ila sun kame Falastinawa a yankuna daban-daban da ke kusa da birnin Quds da nufin ganin sun hana Falastinawa gudanar da gangami a cikin birnin da kewaye.

Wannan mataki dai yana zuwa ne bayan kiran da dukkanin kungiyoyin Falastinawa suka yi ga dukkanin mutanen Quds da sauran yankuna da ke gabar yamma da kogin Jordan na cewa su hadu a birnin Quds a ranar  jiya Juma’a domin bude kofar masallacin babu rahma da ke gefen masallacin aqsa, wanda jami’an tsaron Isra’ila suka kulle shi shi tun a cikin shekara ta 2003.

An zuba daruruwan jami’an tsaron yahudawa a ciki da wajen harabar masallacin mai alfarma, amma duk da haka dubban Falastinawa daga ciki da wajen birnin Quds sun hallara a masallacin, kuma sun bude kofar babu rahma a gaban jami’an tsaron Isra’ila.

A yankin zirin Gaza kuwa yahudawan sun kashe wani matashi bafalastine tare da jikkata wasu dadama.

Tags