Masar Ta Ce Isra'ila Na Kokarin Rarraba Kawunan Shugabanin Afirka
Feb 27, 2019 08:15 UTC
Mataimakin ministan harakokin wajen Masar ya ce a halin da ake ciki yanzu mahukuntan haramtacciyar kasar Isra'ila na kokarin rarraba kawunan kasashen Afirka
Kamfanin dillancin labarai na An-nashra ya nakalto Soad Shalaby mataimakin ministan harakokin wajen Masar yayin da yake gabatar da jawabi a wani taro da ake gudanarwa na kasashen Afirka a birnin Alkahira na cewa wannan rarrabuwar kawuna na zuwa ne ta hanyar amfani da wasu kasashe dake gefen tekun Nile wajen kara matsin lamba ga kasar Masar.
Shalaby ya kara da cewa ganin haka, gwamnatin Masar ta dauki matakin karfafa alakarta da kasar Ethipia domin kiyaye wannan barazana.
A cikin 'yan shekarun baya-bayan nan, rashin fahimta ta kuno kai tsakanin mahukuntan buranan Adis Ababa da Alkahira game da matakin da kasar Habasha ta dauka na gina madatsar ruwa, domin rura wutar fitinar, shugaban haramtacciyar kasar Isra'ila Reuven Rivlin a karon farko ya kai ziyara kasar Ethipia a watan Mayu na shekarar 2018 din da ta gabata.
Tags