India : Adadin Mutanen Da Suka Mutu Sakamakon Gobara Ya Kai 110
(last modified Mon, 11 Apr 2016 06:21:08 GMT )
Apr 11, 2016 06:21 UTC
  • A lokacin fitar da wadanda lamarin ya rusa dasu (hoto AFP)
    A lokacin fitar da wadanda lamarin ya rusa dasu (hoto AFP)

Hukumomi a kasar India sun sanar cewa adadin mutanen da suka rasa rayukan su sakamakon babbar gobara da ta tashi a wani gidan ibada na addinin India dake yankin Kollam na jihar Keralaya ya karu zuwa 110.

Gobara wace ta tashi a jiya Lahadi ta kuma yin sanadin jikkata wasu mutane 390 na daban.

firaministan kasar Narendra Modi ya kai ziyara a wurin da hadarin ya auku, a yayin da ake ci gaba da bincike kan musababin tashin gobarar.

Bayanai sun nuna cewa har yanzu akwai wasu mutanen dake binne a karkashin gidan ibadar da kangayen wasu gidajen da suka wargaje sakamakon tashin gobarar, lamarin da ya sa, mai iyuwa ne za a sami karin mutuwar mutane.

Wasu bayanai na daban dai sun nuna cewa akwai wasu mutane da su kai kayayyakin wasan wuta ba bisa doka ba a cikin gidan ibadar.