Hollande Na Ziyara A Gabas Ta Tsakiya
https://parstoday.ir/ha/news/middle_east-i3946-hollande_na_ziyara_a_gabas_ta_tsakiya
Yau Asabar, shugaban kasar Faransa, François Hollande ke fara wani ran gadi na kwanaki hudu a yankin Gabas ta Tsakiya.
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 16, 2016 04:19 UTC
  • Shugaban Hollande zai Ziyarci kasashen Labonon, Masar da kuma Jodan.
    Shugaban Hollande zai Ziyarci kasashen Labonon, Masar da kuma Jodan.

Yau Asabar, shugaban kasar Faransa, François Hollande ke fara wani ran gadi na kwanaki hudu a yankin Gabas ta Tsakiya.

A yayin wannan ran-gadin shugaba Hollande zai dauko batutuwan da suka shafi yaki da 'yan ta'adan (IS) da kuma matsalar 'yan gudun hijira.

Yau ne ai ake san Hollande zai isa kasar Labonon, kafin daga bisani ya isa kasashen Masar da kuma Jodan.

Kasar Labonon dai na karbar 'yan gudun hijira Syria sama da milyan daya.

kazalika akwai yiwuwar Holande ya gana da wasu daga cikin 'yan gudun hijira Syria dake neman mafaka a kasar Faransa.