Shugaban Kasar Zimbabwe ya goyi bayan Kafa Kasar Palasdinu
Jan 30, 2016 14:05 UTC
Shugaban Kasar Zimbabwe, Robert Mugabe ya bayyana cikakken goyon bayansa na kafa kasar Palasdinu.
Kamfanin Dillancin Labarun Associated Press ya ambato shugaba Robert Mugabe wanda ya ke gabatar da jawabi a wurin taron kungiyar tarayyar Afirka yana mai kiran shugabannin kasashen Afirka da su goyi bayan kafa 'yantacciyar kasar Palasdinu.
Shugaban kasar ta Zimbabwe ya kira yi shugabannin Afirka bayan jawabin da sugaban palasdinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ya yi, yana mai cewa; Muryar Palasdinu tana isowa kunnuwanmu.
Tags