Kasar Masar Ta Hana Ma'aikatan Diblomasian Kasar Qatar 4 Shiga Kasarta
Gwamnatin kasar masar ta hana jami'an diblomasiyar kasar Qatar guda 4 shiga
Gwamnatin kasar masar ta hana jami'an diblomasiyar kasar Qatar guda 4 shiga kasarta. Jaridar yankin gabas ta tsakiya mai suna رأی الیوم wacce ake bugawa a kasar Masar ta bayyana cewa jawami'an diblomasiyar, mata ne su hudu sun shigo kasar ta masar ne da Passport na Diblomasia ba tare da sun dauki Visa daga kasar Bahrain da suka fito ba.
Tun bayan da sojoji suka yiwa gwamnatin Muhammad Mursi ta Ikhwan juyin mulki a shekara ta 2013 ne dangantaka tsakanin masar da Qatar suke tsami, har ya kai ga sun janye jakadun juna daga kasashensu.
Gwamnatin Masar tana zargin Qatar da goyon bayan kungiyar ikhwan wacce sojoji, karkashin shugabancin shugaba Sisi suka kwace iko daga hannunta.